Cutar Sanƙarau ta kashe mutane sama da 100 a Jigawa
Kimanin mutane 100 da suka kasance Ƙananan Yara da keda ƙasa da Shekaru 11 suka rasa rayukansu, sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a Jahar Jigawa.
Rahoto daga Jahar ya nuna cewa ɓarkewar cutar ya fara ne watan da ya gabata, amma lamarin cutar yafi ƙamari a iyakar Najeriya/Niger a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tarihi ne zai maimai ta kanshi, idan Tinubu ya zama Shugaban Ƙasa — Tanko Yakasai
Bincike ya nuna cewa da yawa daga cikin yara sun rasa jin su, a dalilin cutar a sassa daban-daban na Jahar.
Wasu daga cikin ƙauyukan da lamarin yafi yawa ya haɗa da, Mele, Dungundun, da Kanya Arewa, da Dantanoma a Ƙananan Hukumomin Babura, da Gumel, da Maigatari a Jigawa, yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Daily Trust ta ruwaito cewar kimanin mutane 100 suka rasu, a yayinda aka samu mutane sama da 360 masu fama da cutar.
Ƙauyen Dungundun Malam Alkasim Yakubu wanda yayi jawabi akan ɓarkewar cutar, yace sun rasa mutane 19 a kauyen.
Yace lamarin ya fara ne a watan Afrilu, amma cutar ta cigaba da bazuwa a ƙarshen watan daya gabata. Amma lamarin ya ƙara taɓarbarewa makonni da suka gabata
Dayake jawabi, Dagacin Kauyen Mele a Karamar Hukumar Gumel Yusuf Ahmad yace mutane 21 suka mutu, a yayinda 30 suka warke
Comments 1