Daruruwan yara kanana na fuskantar barazanar yunwa da cutar tamowa a sakamakon rikicin yankunan Afar da Tigray da ke kara kamari a kasar Habasha.
Asusun tallafawa kananan Yara na majalissar ninkin duniya wato, UNICEF yaa bayyana damuwar shi kan barazanar yunwa, da yara kanana ke fuskanta a kasar Habasha.
Inda UNICEF ya ce, yara kimanin miliyan hudu ne za su fuskanci tsananin yunwa a sakamakon kazancewar fada a yankin Afar da Tigray, inda asusun ya nemi bangarorin biyu, da su dakatar da fadan, don ceto rayukan wadannan yaran.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Nasarawa za ta rushe gine-gine 200
Daga cikin wasu sama da dubu dari hudu da rikici ya raba da muhallansu, akwai yara da dama, da iyayensu suka yi gudun hijira da su, da ke fama da cutar tamowa inji UNICEF.
Comments 1