Kwana biyu ya rage a kare ci gaba da rijistar masu kada kuri’a da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ke gudanar a karamar hukumar Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa atisayen wanda gaba daya ya kasance cikin kwanciyar hankali da tsari ba tare da cikas ba a ofishin INEC na Kuje da wasu cibiyoyin rijistar, saura kwanaki kadan da cikar wa’adin.
Wadanda suka yi rajistar sun hada da mutanen da ke son yin rijistar sabbin katin zabe na dindindin (PVCs), wadanda katinsu ya bata da kuma wadanda ke son canjawa zuwa wata rumfar zaben.
Sai dai, Mista Yakubu Allawa, jami’in zabe na Kuje INEC (EO), ya ce ofishin na da injinan aiki guda hudu ne kawai ga daukacin yankin, wanda hakan ya sa aikin baya sauri.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/sojoji-sun-murkushe-yan-taadda-60-sun-kubutar-da-yan-matan-chibok-3/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Allawa ya ce wani babban kalubalen da hukumar ke fuskanta shi ne matsalar rashin kyawun tsarin sadarwa, wanda ke dagula harkar a lokacin.
A cewarsa, raba cibiyar rajistar ya taimaka wajen gaggauta aikin da kuma kara rage cunkoso a ofishin.
Ya kara da cewa ana baiwa Nakasassu fifiko da tsofaffi da mata masu juna biyu a yankin.
“Mun dade muna rokon mutane su fito su yi rajista, wannan tunanin na fitowa a minti na karshe ya kamata a daina shi.
“Tun da dadewa mutane sun ki fitowa domin yin rijista kuma yanzu za a rufe sai kara fitowa ake, mutane na yin tururuwa da yawa,” in ji shi.
Sai dai jami’in zaben ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki musamman sarakunan gargajiya da jiga-jigan jam’iyyun siyasa da su hada kai don ganin an samu saukin rajista kafin wa’adin ya kare.
Ya ce hukumar ta shirya tsaf domin yin wannan atisayen idan masu ruwa da tsaki za su ba da hadin kai tare da taimakawa wajen shirya masu rajista a sassansu daban-daban domin yin rajista cikin sauki.
Tun da farko, kafin a raba rajistar, wasu masu rajistar sun bayyana aikin a matsayin mai ban tsoro da ban mamaki, wanda ke fama da jinkiri wajen gudanarwa, tafiyar hawainiya da sauran matsaloli na fasaha.
Don haka suka nemi da a tura karin injuna zuwa unguwannin zabe daban-daban da ke Kuje domin a hanzarta bin diddigin rajistar su kafin cikar wa’adin.
NAN ta kuma ruwaito cewa hukumar ta sanya ranar 31 ga watan Yulin da muke ciki a matsayin wa’adin karshe na gudanar da aikk a fadin kasar nan.
(NAN)