Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan azumin Ramadan
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, Mohammed Abubakar, ya sanar da fara azumin watan Ramadan.
Abubakar ya ce an ga jinjirin watan azumin Ramadan.
KARANTA WANNAN LABARIN:IPAC ta yabawa INEC, masu kada kuri’a da suka yi zabe cikin lumana a Yobe
A wani sako da aka watsa a gidan talabijin na NTA a daren Laraba, Sarkin ya ce musulmin kasar nan su fara azumin ranar Alhamis 23 ga watan Maris.
A wani labarin kuma:Zaɓen Najeriya: Burtaniya za ta haramtawa masu siyan kuri’u da masu adawa da dimokuradiyya biza
Babbar hukumar Biritaniya a Najeriya ta yi Allah-wadai da kalaman kabilanci da addini da wasu jiga-jigan al’umma da na siyasa suka yi a yayin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 18 ga watan Maris.
Wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Laraba ta ce Birtaniya ta lura da tashin hankali, da kuma dakile masu kada kuri’a a wurare da dama na kada kuri’a.
Comments 1