Da Ɗumi-Ɗuminsa: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga Ƴan Najeriya kan ƙarancin kuɗi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi jawabi a yau, Alhamis, a fadin kasar.
Mai taimaka wa shugaban kasa, Bashir Ahmed ne ya bayyana hakan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Karancin Naira: Kun Sha wahala sosai, ku kori APC kawai – Saraki ga Ƴan Najeriya
Ya wallafa a shafinsa na twitter da yammacin Laraba cewa: “Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da shirye-shiryen kasa gobe 16 ga Fabrairu, 2023 da karfe 7 na safe.
“An umurci gidajen talabijin, gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su hada kai da ayyukan sadarwar NTA da Rediyon Najeriya don watsa shirye-shiryen.”
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara tabarbarewar karancin kudaden da ake samu na sabbin kudin Naira.
‘Yan kasar da suka fusata sun yi ta matsin lamba a ranar Laraba, inda aka gudanar da zanga-zangar lokaci guda a duk fadin kasar.
Baya ga hare-haren da ake kai wa wasu cibiyoyin hada-hadar kudi, an kuma samu asarar rayuka yayin da hukumomin tsaro ke kokarin dakile tarzomar.
Idan za’a tuna kafin wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu, shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su bai wa gwamnatinsa mako guda domin warware matsalolin da ke tasowa sakamakon karancin kudin Naira.
Sai dai da wa’adin ya kare, kuma babban bankin Najeriya CBN ya nanata cewa babu gudu babu ja da baya, sai aka yi shiru daga fadar shugaban kasa.
Kokarin da wasu gwamnatocin Jihohi suka yi na neman jin ta bakin kotun koli bai haifar da da mai ido ba domin kuwa CBN ya tsaya tsayin daka kan matsayinsa duk da umarnin da kotun kolin ta bayar.
A wani labarin kuma: Ba mu ajiye wa wani yanki kujerar shugaban kasa ba — Dattawan Arewa
Kungiyar dattawan Arewa NEF, ta bayyana cewa yankin arewacin kasar bai tanadi shugabancin kasa ga wasu yankuna a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a wajen taron dattawan Arewa da aka yi a Abuja, ya yi ikirarin cewa har yanzu Arewa na da sauran shekaru hudu da za ta yi mulki domin daidaita kudancin Najeriya.