Kungiyar kwallon kafa ta Qatar, Al Sadd ta sanar da cewa Barcelona ta biya kudin siyan dan wasan Xavi Hernandes kuma yanzu ya koma kungiyar ta Spain a matsayin koci.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter ranar Juma’a.
Sanarwar ta kara da cewa, Hukumar gudanarwar AlSadd ta amince da komawar Xavi zuwa Barcelona bayan biyan kudin sayen dan wasan da aka tanada a kwantiragin.
Har yanzu kulop din Barcelona bashi da kogi tun bayan korar Ronald Koeman.
Barcelona ta sanar da cewa Barjuan zai ci gaba da zama a matsayin har sai an sami wanda zai maye gurbin Koeman.