Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta sanar da naɗa Sergi Barjuan a matsayin Manajan ta, biyo bayan korar Ronald Koeman.
Barjuan ya kasance yana jagorantar ƙaramar ƙungiyar ta Barca B kafin wannan sabon muƙamin.
Zai kasance a muƙamin Manaja kafin Ƙungiyar ta ɗauko hayar cikakken manaja wanda zai gaji Koeman.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kano: Yan Sanda Sun Kama wasu Masu laifi 59
“Ƙungiyar Barcelona ta sanar da Sergi Barjuan, kocin Barca B, inda zai cigaba da jagorantar Babbar Ƙungiyar,” kamar yadda ƙungiyar ta sanar a shafin ta na yanar gizo a ranar Alhamis.
“Muƙamin shi zai ƙare da zarar anyi hayar wanda zai cigaba da jagorantar ƙungiyar, kuma zai gaji Ronald Koeman.
Shugaban Ƙungiyar, Joan Laporta zai sanar da Sergi Barjuan a matsayin shugaban Babbar Ƙungiyar kafin wasan horas wa a ɗakin taro na Ciutat Esportiva.
“Sergi Barjuan zai yi jawabi ga Kafafen Yaɗa Labaru a ranar Alhamis da misalin karfe 1:00 na rana a ɗakin ƴan jarida ba Ciutat Esportiva domin tattaunawa da Joan Laporta.