Babban Sufeto-Janar na Ƴan sandan Ƙasar nan Alƙali Usman Baba ya Isa wurin da gini ya rufta a yankin Ikoyi na Jahar Lagos.
A ranar Talata Sufeto-Janar ɗin , ya zo da motocin ƴan sanda da jami’an tsaro da yawa a wurin da lamarin ya faru.
Da isar sa wurin, ya tafi kai tsaye zuwa farfajiyar wurin, kuma har yanzu bai yiwa Manema labaru jawabi ba akan lamarin, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

KARANTA WANNAN LABARIN:
Ruftawar Bene: Gwamnan Legas Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar Kula Da Gine-Gine Na jihar
A wani Labarin kuma
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayar da umarnin dakatar da babban manajan hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas Mista Gbolahan Oki.
Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta gano abin da Akayi Wanda bai dace ba, kuma za ta hukunta wadanda ake tuhuma a ruftawar wani bene mai hawa 21 da ya ruguje a Ikoyi na jihar Legas a jiya Litinin.
Gwamnan, a matakin farko, ya bayar da umarnin dakatar da Babban Manajan Hukumar Kula da Gine-gine ta Jihar Legas (LASBCA), Mista Gbolahan Oki, Wanda ya kadance masani ne a fannin gine-gine, daga aiki nan take. Kuma har sai baba ya gani
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Legas Gbenga Omotoso ya rabawa manema labarai a jihar.
Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Legas na kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki rugujewar ginin bene mai hawa 21 da ke kan titin Gerrard, a garin Ikoyi dake jihar”
“Mambobin kwamitin za a zabo su ne daga Cibiyar Nazarin Gine-gine ta Najeriya (NIA), Cibiyar Injiniyoyi ta Kasa da Kasa, da sauran kwararrun a fannin da abun ya shafa”
“Kwamitin zai binciki abubuwan da suka faru na nesa da na kusa, tare da bayar da shawarwari kan yadda za a hana afkuwar lamarin a nan gaba. Binciken ba ya cikin binciken cikin gida da gwamnati ke gudanarwa” inji sanarwar
“Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce tabbas gwamnati za ta gano abin da ya faru kuma za ta hukunta wadanda ake tuhuma.” a cewar Sanarwar.
Comments 1