Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana zaben Gwamnan Anambra a matsayin wanda bai kammala ba (Inconclusive).
Farfesa Florence Obi, jami’ar da ke kula da zaben ce ta bayyana hakan a babban ofishin INEC da ke Awka, babban birnin Anambra, a safiyar ranar Litinin.
Ta ce sakamakon zaben kawo bai kawo karshe ba saboda babu zabe a karamar hukumar Ihiala da ke jihar.
Da take tabbatar da matakin da ta dauka kan dokar zabe, Obi ta ce za a sake gudanar da zaben a Ihiala ranar Talata.
Farfesa Chukwuma Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya samu kuri’u mafi girma a zaben na ranar Asabar.