Akwai yawaitar Jami’an tsaro a Majalisar Dokokin Jahar Filato.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar da misalin ƙarfe 5:30 na safe a ranar Alhamis, hanyar da zata kai mutum zuwa Majalisar dake kan hanyar John Mark Samci a Jos, Babban birnin Jahar, an canjawa motoci hanya zuwa wasu hanyoyin.

KARANTA WANNAN LABARIN: Sauyin Yanayi Na iya Haifar Bakin Haure A Najeriya Miliyan 9.4 Nan Da Shekarar 2050 – Bankin Duniya
Wani mazaunin kusa da Majalisar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos a ranar Alhamis, yace “na tashi da safe naga ƴan sanda da sauran jami’an tsaro a ko’ina. Ba zamu iya fita da ababen hawan mu ba, domin an kulle hanyoyin. Abun damuwa ta shine in kai ƴaƴana zuwa makaranta. Muna nan zaune a wuri guda.”
Haka zalika, an gano cewa an kai jami’an tsaro domin magance karya doka da oda bayan an tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jahar.
Comments 1