Kwamishinan Ƴan Sandan Jahar Lagos Hakeem Odumosu ya Isa wurin da gini ya rufta a yankin Ikoyi na Jahar a ranar Litinin.
Kwamishinan a ranar Laraba ya iso wurin da tawagar ƴan sanda a cikin mota, zuwa wurin da lamarin ya shafa.
A lokacin zuwan sa, ya tafi kai tsaye zuwa wurin da lamarin ya shafa, kuma ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai yiwa Manema labaru jawabi ba.

KARANTA WANNAN LABARIN: Jita-jitar Ƙarancin Man Fetur: NNPC tayi gargaɗin rige-rigen sayen Man Fetur, duk ƴan kasuwa sun ƙara farashi
Ya kuma sha alwashin yiwa Manema labaru jawabi akan ziyarar.
A ranar Laraba da safe an ceto gawa guda biyu a cikin ginin daya rufta, wanda adadin waɗanda suka mutu yakai mutane 22.
Benen mai hawa 21 ana ginin shi a lokacin da ya karye ya faɗo ƙass a ranar Litinin a Ikoyi.
Masu ceto mutane a ranar Laraba sun ceto gawa 22, daga cikin wanda aka ceto akwai mutum 9 da suka rayu, amma masu ginin suna jin tsoron akwai da yawan mutane a cikin waɗanda ginin ya rufta dasu.