Kasuwar Ƙauye dake Kubwa ta yankin Bwari Abuja, a halin yanzu tana cigaba da cin wuta.
A ƙalla mutane 3 suka rasa rayukansu a gobarar, a sa’ilinda mutane da dama suka ji raunuka.
An lura da cewar, fashewar tankar mai itace ta haddasa gobarar a wani shago kusa da Babbar Kasuwar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Naji kunya da bamu yi hangen kai hari a Makarantar NDA ba — inji Irabor
A lokacin da aka tuntuɓe shi, muƙaddashin Daraktar Hukumar Bayar da A gajin gaggawa ta Babban Birnin Tarayya Abuja Mrs. Florence Wenegieme ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ƙara dacewa ɓata gari tuni sun mamaye wurin da gobarar ke ci, kuma suna hana masu yaƙi da gobarar daga cigaba da aikin su.
Tace “lamarin ya faru babu nesa dasu. Bazan iya gaya maku dalilin gobarar ba, amma zan iya cewa mutane 3 sun rasu, kuma har yanzu bamu ɗauki gawarwakin ba, sabudda ɓata gari sun mamaye wurin. Kuma sunƙi baiwa mutanen mu gudanar da aikin su, kuma tuni sun tsaya wani wuri suna jiran Ƴan sanda su ƙara so.
Comments 1