Tsohon Kwamishinan Ƙasa da Gidaje na Jahar Oyo Mr. Ajiboye Omedewu ya zama shugaban jam’iyyar APC a Jahar.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar Omedewu ya zama shugaban jam’iyyar a wani zaɓe da aka gudanar a filin wasan ƙwallon ƙafa na Obafemi Awolowo dake Oke-Ado na Ibadan a ranar Asabar.
Kasancewar shi shugaban jam’iyyar ya biyo bayan wani ƙudiri da Wani ɗan Majalisa na Jahar Dokun Odebunmi ya gabatar akan buƙatar dake akwai na tabbatar da sabbin shugabannin jam’iyyar a matsayin shugabannin jam’iyyar.

KARANTA WANNAN LABARIN: NECO na bin jahohi 6 bashin Naira Biliyan 1.8na kuɗaɗen jarabawar ɗaliban su — Cewar Wushishi
Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Kahinde Subair ya goyi bayan ƙudirin.
Zaɓen shugabannin ya samu jagorancin Sakataren Kwamitin Shirya zaɓen Shugabannin jam’iyyar APC na Jahar Abdullahi Bello.
Bello, wanda shine shugaban jam’iyyar APC a Jahar Kogi ya bayyana cewa an cimma matsaya na gudanar da zaɓen ta hanyar sasanci.
Kwamitin ya kuma karanta sunayen waɗanda suka samu nasarar lashe zaɓen, inda daga bisani aka amince dasu.
Zaɓen shuwagabannin wanda ya gudana a ranar Asabar da rana, ya samu halartar Jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa-INEC.