Ƙasar Amurka ta bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan siyasar Najeriya zasu rasa Bizar shiga kasar Amurka idan aka same su da laifin maguɗin zaɓen da za a gudanar a jihar Edo.
Kamar yadda Sahara Reporters ta rawaito cewa, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa shi ne na farko ciki jerin sunayen wanda ƙasar Amurka ta kafawa takunkumin hana shiga ƙasar.
Gwamnan Kano Abullahi Umar Ganduje, gwamnan Kogi Yahaya Bello na daga cikin wanda Amurka ta hana shiga cikin ƙasarta.
Daga wani ɓangaren kuwa gwamnan El-Rufa’i na Kaduna hukumar gudanarwa ta ƙasar Amurka ta soke Bizar ta da bawa gwamnan domin shiga ƙasar.
An dakatar da El-Rufa’i da shiga ƙasar Amurka tun shekara ta 2010.
Hukumomi daga ƙasar Amurka sun bayyana cewa za a samu ƙarin ‘yan siyasar da za a hana shiga ƙasar Amurka ɗin da zarar an same su da laifukan maguɗin zaɓe a jihar Edo.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda hukuncin ya shafa an aike musu da saƙon kar-ta-kwana ta email ko kuma lambobin wayarsu.
Sanarwar da hukumar gudanarwa ta ƙasar Amurka ta fitar a ranar Litinin, wanda Morgan Ortagus ya sanyawa hannu, ta ce wanda hukuncin ya shafa an kama su da laifukan kawo wa dimokuraɗiyya naƙaso a Najeriya.