Hukumar zaben ƙasar Kenya ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, da kashi 50.49 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Hukumar zaɓen ta sanar da sakamakon zaben ne a yammacin Litinin din nan.
An gudanar da zaɓen ne a ranar Talatar da ta gabata wato 9 ga watan Agustan 2022.
Gara Sun Cinye Takaddun Da Ke Dauke Da Bayanan Yadda Muka Kashe Naira Billiyan 17 — Hukumar NSITF
A yayin da yake jawabi bayan sanar da nasararsa, William Ruto ya ce “Yammaci ne mai matuƙar daɗi, cike da farin ciki.
Tazarar da ke tsakaninsa da abokin fafatawarsa Raila Odinga ba shi da yawa, inda shi Odingan ya samu kashi 50.4 na yawan ƙuri’un.
An jinkirta sanar da sakamakon saboda zarge-zargen maguɗi da aka dinga yi wa ɓangaren Odinga.
Huɗu daga cikin mambobin hukumar zaɓen bakwai sun ƙi su amince da a fitar da sanarwar sakamakon, suna cewa an yi maguɗi.