DA ƊUMI-ƊUMI: Rikicin Iyaka ya haddasa Gobara mai tsanani a Delta
Al’ummar Aladja da ke karamar hukumar Udu ta jihar Delta a safiyar Juma’a, sun yi korafin cewa al’ummar Ogbe-Ijoh da ke karamar hukumar Warri ta Kudu-maso-Yamma sun yi ta harbe-harbe a yankin su (Aladja).
Jaridar DAILY POST ta rahoto cewa hakan ya zo ne a daidai lokacin da wa’adin kwanaki 7 da suka baiwa kwamitin shata iyaka na jihar domin maye gurbin gine-ginen da ake zargin an lalata a yankin ya zo karshe.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kori Shugaban Kasuwa kan Gini ba bisa ƙa’ida ba
Wani dan kabilar Aladja, Kwamared Ighotegwolor Bezi ya yi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu a Warri.
Ya ce, “Babu wanda ya samu rauni ko kuma ya mutu a halin yanzu, amma wurin yana cikin tashin hankali.
“Muna kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa, ciki har da Gwamnatin Jihar Delta da su kawo dauki ga al’ummar Aladja kafin lamarin ya kure.”
Sai dai ya yi gargadin cewa al’ummar Aladja ba za su nade hannayensu ba su bar maharan su saki.
Idan za a iya tunawa, ‘yan kungiyar masu fafutukar kare muradun masarautar Ogbe-Ijoh Warri sun yi zargin lalata gine-ginen su ba bisa ka’ida ba a yayin da suke aikin tantance layukan kan iyaka.
A wani labarin kuma: Ba zamu Amince Da Yajin Aikin ASUU — Manyan Limaman Coci Sun Caccaki Gwamnatin Tarayya
Limamin cocin Katolika na Najeriya sun caccaki gwamnatin tarayya a kan matakin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta dauka tun watanni bakwai da suka gabata.
Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU da su samar da hanya mafi inganci don magance rikicin domin sake bude jami’o’in gwamnati.