Da ɗumi-ɗuminsa: Kwankwaso ya isa gidan Shekarau domin tattaunawar ƙarshe kan koma wa NNPP
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya isa gidan Sanata Ibrahim Shekarau dake Kano domin tattaunawa ta ƙarshe kan yarjejeniyar komawa sabuwar Jam’iyya NNPP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje Ya Naɗa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano Na Riƙo
Ana saran Shekarau zU sanar da canja sheƙar sa daga Jam’iyyar APC a ranar Asabar, amma aka ɗaga hakan kan wani dalili da ba’a san shi ba.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar Juma’a ya ziyarci Shekarau domin ya fasa canja Jam’iyyar, bayan haka dukkanin su aka kira su a Abuja, amma Shekaru yaƙi zuwa taron, bayan yace ba’a fadar Shugaban Ƙasa bace ta kira shi domin yin sulhun.
Amma a ranar Lahadi, Kwankwaso shima Tsohon Gwamnan Jahar ya isa Mudunbawa gidan Shekarau dake Kano tare da wasu Jiga-Jigan NNPP domin tattaunawa ta ƙarshe akan shirin sa na komawa Jam’iyyar wanda zai faru a ranar Litinin.
Majiyoyi daga ɓangaren Shekarau ta shaidawa Daily Trust cewa tuni an kammala batun canja Jam’iyyar a yayinda dukkanin makusantan Gwamna a Ƙananan Hukumomi 44 sun amince domin komawa a NNPP.