Da Ɗumi-Ɗuminsa: Malami, Tallen sun halarci taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa
Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar Mata Pauline Tallen a ranar Laraba sun halarci taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa na sati-sati.
Ministocin wanda suka janye daga Takarar Gwamna a Jahar Kebbi, da Kujerar Sanata, sun halarci taron da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke jagorant daya wakana a ɗakin taro na Villa dake Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum guda ya mutu, wasu sun jikkata yayin da Masu zanga-zanga suka kutsakai Ofishin yan sanda a Ghana
Jaridar The PUNCH tunda farko ta bada rahoton cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarni ga dukkanin mambobin Majalisar Zartaswa na Ƙasa dasu sauka daga muƙamin su.
A ranar Juma’a, ya gudanar da taro domin bankwana da Ministoci guda 10. Dukkanin su sun halarta sai dai banda Ƙaramin Ministan Ilmi Chukwuemeka Nwajiuba.
Ministocin da tuni suka canja ra’ayin su na yin Takara sun haɗa da Malami, da Tallen, da Ministan Ƙwadago da Ayyukan yi Dr. Chris Ngige wanda ya nemi Kujerar Shugaban Ƙasa.
Kafin taron ya fara, Majalisar ta yi shiru na tsawon mintuna domin girmama Tsohon Ministan Sadarwa a ƙarƙashin Mulkin Babangida Olawale Ige wanda ya mutu yana da shekaru 83.
Waɗanda suka halarci taron Majalisar Zartaswa sun haɗa da Farfesa Yemi Osinbajo, Shugabar Ma’aikata ta Ƙasa Dr. Folasade Yemi-Esan, Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari, da Mai bada Shawara akan tsaro, Manjo-Janar Babagana Munguno (mai ritaya), sai Ministoci.