Da ɗumi-ɗuminsa: NFF ta naɗa José Peseiro a matsayin Shugaban Masu Horas da Super Eagles
Hukumar Kula da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa a ranar Asabar ta sanar da naɗa Mr Joeé Santos Peseiro a matsayin sabon shugaban masu Horas da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na bar APC sabudda Cin Hanci da yayi yawa a cikin ta — Cewar Mai Neman Ɗan Majalisar Wakilai a Osun
Zai fara aiki nan take, bayan ya sanya hannu akan yarjejeniya tsakanin NFF da Mr Peseiro.
José Vitor dos Santos Peseiro a watan da ya gabata ne, ya kasance ɗan Ƙasar Portugal daya ke da masaniya sosai akan Horas da Ƴan Wasa a Nahiyoyi da suka haɗa da Europe da Asia da Afrika da Amerika ta Kudu.
Yana da Digiri akan wasanni da kuma ƙwarewa wajen Jagorantar Ƴan Wasa, zai Jagoranci Super Eagles karo na farko.