Babbar kotun masana’antu ta yi umarni ga kungiyar malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU da ta janye yajin aikin da take yi.
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta shigar da kungiyar kara a gaban kotun.
A zaman da aka yi a ranar Litinin kotu ta ce ranar Larabar nan za ta yanke hukunci.