Mambobin ƙungiyar ƙwadago da wasu mazauna a jahar Ogun a ranar Laraba, sun toshe hanyar Sanga Ota, wani sashe na Babbar hanyar Lagos-Abeokuta a wata zanga-zanga da aka gudanar sabudda rashin kyawun hanyar.
Masu zanga-zangar sun rufe hanyar Sanga-Ota a ƙaramar hukumar Ado-Odo/Ota ta jahar, daga wajen tsayawar mota na Joju a lokacin zanga-zangar.
Masu zanga-zangar sun buƙaci Gwamnatocin tarayya da jaha dasu gano hanyoyin da za’a kawo ƙarshen rashin kyawun hanyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: NIN-SIM: MTN Na Jayayya Kan Sabuwar Dokar NCC
Haka zalika, masu zanga-zangar sun ɗauki takardu da dama masu rubuce-rubuce kamar haka “ka gyara mana
hanya nan bada jimawa ba” hanyoyin mu tarko ne na mutuwa, babu hanya mai kyau babu biyan haraji, da dai sauransu.
Dayake jagorantar zanga-zangar, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Jahar Emmanuel Bankole, yace ƙungiyar ta yanke shawarar nuna rashin jindaɗin ta sabuda halin ko in kula da gwamnati ke nunawa, bayan ziyarar Ministan Ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ga hanyar, kuma baiyi komai akan hanyar ba.
Masu zanga-zangar sun kuma yi gargaɗin kulle jahar Ogun idan ba’a fara ba, nan da kwanaki 21.