Ƴan bindiga sun kai hari ga Al’ummar Te’egbe dake ƙaramar hukumar Bassa ta Jahar Filato, tare da kashe mutane da dama.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar dukiya da dama data jiɓance su duk sun ƙone ta, a yayinda da dama daga cikin jama’a suka samu raunuka da dama a lokacin kai harin, wanda ya faru da sanyin safiyar Juma’a.
Mai magana da yawun ƙungiyar Matasa ta Miango Nuju Bitrus ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch a ranar Juma’a a Jos.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bakar Fata Mace Ta Farko ‘Yar Kano Ta Karya Tarihi A Jami’ar Landon
A cewar Bitrus, bincike da ceto mutane ya fara kankama wanda ake cigaba da gudanarwa.
Ya ƙara dacewa a halin yanzu, mutane 10 suka kashe, kuma an kai gawar su a wurin ajiye gawa.
Bitrus yace ” a daren jiya, wata mummunar rana ta sake afkuwa, inda ƴan bindiga suka kai hari ga ƙauyen Te’egbe tare da kashe mutane da dama, da jikkata wasu.sun kuma ƙone gidajen su.
Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ubah Ogaba, ba’a same shi ba domin jin ta bakinsa akan lamarin, har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.