Da ɗuminsa: Buhari ya naɗa Doyin Salami a matsayin Babban mai bashi shawara akan tattalin arziki
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Dr Doyin Salami a matsayin Babban mai bashi shawara akan tattalin arziki.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai bashi Shawara kan Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina ya fitar.
- KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Aike Da Tawagar Ta’aziyya Jihar Kano Tare Da Wasika
Ɗan shekaru 59 ana saran zai magance dukkanin wasu matsaloli akan tattalin arzikin cikin gida, tare da kai su ga Shugaban Ƙasa, tare da duba dukkanin wasu cigaba a wasu ƙasashe, tare da ɓullo da wasu dabaru da zasu inganta tattalin arziki.
Salami zai kuma ɓunkasa, tare da bada shawara ga Shugaban Ƙasa akan shirye-shiryen da zasu inganta tattalin arziki, gami da samar da ayyukan yi, da magance talauci da sauran su.