Da Ɗuminsa: Gobara ta kama a Rukunin wasu Gidaje a Ikoyi
Wata Gobara ta barke a wasu rukunin gidaje akan hanyar Ilabere dake Ikoyi ta Jahar Lagos da farkon safiyar ranar Laraba.
Babban Sakataren Ma’aikatar Bada Agajin Gaggawa na Jahar Lagos Dr Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Labarin Bidiyon kai hari kan Coci a Zamfara Ƙarya ne – Rundunar Yan sandan
Yace Jami’an Hukumar bada agajin gaggawa ta LASEMA an tura shi a wurin da lamarin daya faru, daga lokacin da aka kai rahoto.
Oke-Osanyintolu ya ƙara dacewa, LASEMA na aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar Kashe Gobara ta Jahar Lagos domin magance yanayin wutar.
“Hukumar tuni ta tura da shirin kai agajin gaggawa zuwa wurin. Hadakar Jami’an Hukumar LRT da na Hukumar Kashe Gobara ta Jahar Lagos suna bakin ƙoƙari domin kashe gobarar, wadda a halin yanzu take Cigaba da cin Dukiyoyi”, Inji Sanarwar.
Har yanzu dai babu rahoton kashe wani ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Comments 1