Da Ɗuminsa: Gwamnan Jigawa ya naɗa sabon Sarkin Dutse
Gwamnan Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse
Gwamnan JIhar Jigawa Badaru Abubakar ya amice da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse, domin maye gurbin mahaifinsa wanda ya rasu a makon jiya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kwanaki bakwai ya yi yawa– Wani Sanata ya yi tsokaci ga Buhari kan ƙarancin takardun kuɗi
Wannan ya biyo bayan shawarar da masu zaben sarki daga Masarautar Dutse suka gabatar, wadan ya amince da nadin Hameem ba tare da wata hammaya ba.
Wata sanarwa daga Majalisar Sarki tace an gabatar da sunan Hameem tare da wasu ‘yayan sarki biyu, amma sai aka zabe shi domin maye gurbin mahaifinsa.
Sanarwar tace daga yau 5 ga watan Fabarairu, gwamna Abubakar ya amince da Muhammad hammen Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tururuwa zuwa garin Dutse domin gabatar da ta’aziyar rasuwar Sarki Sanusi wanda akasarin jama’a ke jinjina masa saboda adalcinsa da jajircewa da kuma taimakon jama’a lokacin da yake rike da Masarautar.
Dubban mutane ne suka halarci jana’izarsa da akayi a garin Dutse bayan rasuwar da Allah ya masa a wani asibiti dake Abuja.
A wani labarin kuma:Zaɓen 2023: Tambuwal ya rasa wani hadimin sa ga APC
Alhaji Abubakar Kwaire, mai ba Gwamna Aminu Tambuwal shawara na musamman ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin zaben 2023 a jihar.
Kwaire, a cewar wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai baiwa Sanata Aliyu Wamakko, shawara ta musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ya fitar, ya samu tarba daga dan takarar gwamnan jihar na APC, Alhaji Ahmad Aliyu a Sokoto.