Mambobin Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso yamma a ranar Talata, sunyi taro a Lagos domin tattaunawa akan wasu al’amura da suka shafi tsaro, saka hannun jari, sa sauran wasu al’amura da suka shafi yankin.
Gwamna Babajide Sanwa-Olu ya tarbi Gwamnonin a gidan Gwamnatin Jahar, kwanaki uku bayan ƴan ta’adda sun kai hari a gidan yari na Ibadan, tare da sakin mazauna wurin.
Gwamnoni biyar da suke ƙarƙashin ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso yamma suka halarci taron, wanda ya fara tun ƙarfe 4:30 na rana a cikin sirri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje ya nemi amincewar Majalisa domin ciwo bashin biliyan 20 dazai gudanar da wasu ayyukan raya ƙasa
Gwamnan Jahar Oyo Seyi Makinde ya samu wakilcin mataimakin sa Mr Rauf Olaniyan.
Bayan mintoci 90, Gwamnonin sun tashi daga taron, ba tare da sanar da cikakkun bayanai akan al’amuran da suka tattauna ba.
Dayake jawabi ga Manema labaru, Shugaban Ƙungiyar kuma Gwamnan Jahar Ondo Rotimi Akeredolu ya bada taƙaitaccen bayani akan tattaunawar su, inda yace daga cikin abinda tattaunar tafi maida hankali shine akan tsaro.
Akeredolu yace akwai kuma tattauna akan ƴan ƙungiyar Oduduwa, inda yace ƙungiyar bata son fitar da bayanai akan abinda ta tattauna duka.
Gwamnonin sun kuma bar gidan Gwamnatin Lagos bayan jawabin ga Manema labaru