Akwai fargaba a tsakanin Ɗaliban Najeriya dake karatu a Jami’o’i akan rashin sanin abinda zai fito daga taron da mambobin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ke gudanarwa.
Majiyar mu ta The PUNCH ta ruwaito cewa, a yayin taron ana tunanin a ɗauki matsaya akan tafiya yajin aiki.
Haka zalika, a halin yanzu mambobin gudanarwa na Kungiyar ASUU suna gudanar da taro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilan da suka sanya APC zata faɗi zaɓen Gwamnan Ekiti — Inji PDP
Shuwagabancin gudanarwa na ASUU ya ƙunshi Shuwagabanni na Ƙasa, na shiyyoyi da sassa.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Shugaban ASUU reshen OAU Dr Adeola Egbedokun yace har yanzu ba’a cimma matsaya ba ya zuwa ƙarfe 08:50 na dare.
“Babu wani abu da za’a tabbatar,” ya bayyana, yana mai cewa har yanzu ba’a sanar da yajin aikin ba.
Ƙungiyar dai ta bayyana damuwar ta akan kasawar Gwamnatin Tarayya na cika wasu alƙawurra da tayi a shekarar 2009.
ASUU dai a watan Nuwamba 15 na shekarar 2021 ta baiwa Gwamnatin Tarayya Makonni 3 akan gaza cika alƙawarin su.
Comments 1