Waɗannan ƙasurguman ƴan bindiga da ake nema ruwa jallo sun haɗu da gamon su, bayan Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya, ƙarkashin shirin Operation Hadarin Daji, ya kai sama me a wani bayanan sirri daya samu, inda ya babbake su a dajin Gusami da ƙauyen Tsamre a Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji a daren daya gabata.
Wannan hare-haren da jirgin ya kai an gudanar dashi da sanyin safiyar Asabar a ranar Asabar, inda ya kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan nan Auta, da Rugar sa, kamar yadda kamfanin PRNigeria ya ruwaito.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ƴan ta’adda da dama sun taru domin binne shi, inda jirgin ya ƙara kai hari, tare da kashe adadi mai yawa da har yanzu ba’a tabbatar ko nawa ba ne..
KARANTA WANNAN LABARIN:;Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Rashin Tsaro A Nigeria Da Barazana Ga Dimokuradiyya A Kasar
Wani Jami’in sirri na Soji ya shaidawa PRNigeria cewa, wannan hari da jirgin ya kai ga ƴan ta’addan da suka ɓoye a ƙarƙashin itatuwa kusa da wurin, ya sanya aka kashe su da yawa.
” A yanzu dai, bamu san inda manyan ƴan ta’addan nan da suka haɗa da Alhaji Nashamu, da Shingi, da Halilu suke, wanda ƙila sun ɓoye ko sun ruga,” Inji jami’in.
PRNigeria ta kuma shaida daga wata majiya a ɓangaren soji cewa, wannan hare-hare da Jirgin Rundunar sojin sama ya kai a ƴan lokacin nan, ya yi wa ƴan bindiga ɓanna, inda ya kashe Shuwagabancin su da mabiyan su.
“Wannan kai hare-hare sun tabbatar wa ƴan ƙasa irin jajircewa da namijin ƙoƙarin soji da sauran Hukumomin tsaro na kawo ƙarshen ƴan bindiga ƙarshe nan bada jimawa ba.
“Ƴan ƙasa musamman mutanen dake kusa da waɗannan al’ummomi dasu cigaba da bayar da sahihan bayanai da zasu taimaka wajen magance wannan matsala data zama barazana ga rayuwar su,”inji shi.