Daga: Abbas Yakubu Yaura
Mai shari’a Adeyemi Ajayi na babbar kotun birnin tarayya ya bayar da umarnin a tsare tsohon Akanta Janar na tarayya Ahmed Idris da wasu mutane biyu a gidan gyaran hali da tarbiyya na, Kuje.
Mai shari’a Ajayi ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Idris da wadanda ake tuhumarsu a Kuje har zuwa lokacin da za a saurari bukatar neman belinsu ranar 27 ga watan Yuli.
KARANTA WANNAN LABARIN:https://dimokuradiyya.com.ng/hatsari-ya-hallaka-mutane-30-yayi-sanadin-%c6%99onewar-motoci-a-kaduna/
Hukuncin ci gaba da tsare shi ya biyo bayan gurfanar da tsohon Akanta Janar din ne a ranar Juma’a da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi.
Sauran wadanda ake tuhumar su ne Godfrey Olusegun Akindele, Mohammed Kudu Usman, da Gezawa Commodity Market and Exchange Ltd.. Ana tuhumar su da tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata da laifin zamba da ya kai Naira biliyan 109, 485,572,691.9.
EFCC ta yi zargin cewa Ahmed Idris, a tsakanin watan Fabrairu zuwa Disambar shekarar 2021 a Abuja, kasancewarsa ma’aikacin gwamnati ta dalilin matsayinsa na babban Akanta Janar na Tarayya ya karba daga hannun Olusegun Akindele,kimanin jimillar kudi Naira (Biliyan Goma Sha Biyar)da Miliyan Dari Da Talatin da Shida, Dubu Dari Biyu Da Ashirin Da Daya, daNaira Dari Tara Da Ashirin Da Daya Da Kobo Arba’in Da Shida) 15,136,221,921.46
Wanda Cewar Olusegun Akindele ya koma Dalar Amurka wanda kuma kudin bai zama wani bangare na ba.
Ladan ku na halal amma a matsayin dalili na hanzarta biyan kashi 13% na rarar man fetur ga jihohi tara (9) da ke hako mai a cikin Tarayyar.
Ta hannun ofishin Akanta Janar na tarayya, kuma ta aikata laifin da ya sabawa sashe na 155 na dokar aikata laifuka ta 532 na kundun tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1990 wanda kuma ke da hukunci a karkashin wannan sashe.
“Kai, Ahmed Idris a lokacin da kake matsayin Akanta Janar na Tarayya da Godfrey Olusegun Akindele yayin da kake Mataimakin Babban Akanta Janar na Tarayya tsakanin Fabrairu da Nuwambar shekarar 2021, a Abuja a sashin shari’a na Abuja. Babban Kotun Babban Birnin Tarayya, a irin wannan matsayi, da aka ba wa wasu kadarori, Naira Miliyan Dari Uku da Tasa’in) ya aikata laifin zamba a cikin dukiyar da aka ambata, a lokacin da kuka karɓi wannan adadin daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta hannun Godfrey Olusegun Akindele yana kasuwanci da sunan salon Olusegun Akindele & Co., kuma ka aikata laifin da za a hukunta ka a karkashin sashe na 315 na kundin dokar aikata laifuka ta 532 na kundun tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1990”.
Rotimi Jacobs SAN lauyan masu gabatar da kara yayin da Cif Chris Uche SAN, ke wakiltar wanda ake tuhuma na daya (Idris).