Kotu ta kori shari’ar da ɓangaren Aregbesola ya shigar akan zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar APC
Mai Shari’a Nathaniel Ayo-Emmanuel na Babbar Kotun Tarayya dake Osogbo a ranar Laraba, ya watsar da ƙarar da aka shigar wanda wasu Fusatattun ƴan Jam’iyyar APC suka yi, akan zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar APC a matakin Mazaɓu a Jahar Osun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum biyu Sun Mutu, Yayin da Mota ta kwacewa Wani Direban a Abeokuta
Ayo-Emmanuel a yanke Shari’ar, wanda ta ɗauki mintuna awa ɗaya, da mintuna 30 ya bayyana cewar al’amuran da suka shafi zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyu na cikin gida ne, saiya kori shari’a.
A wani Labarin kuma
An tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hadarin mota da ya faru a jihar Ogun da safiyar Laraba..
Hadarin daya tilo wanda ya hada da wata motar bas ta Mazdes ta faru ne da misalin karfe 08:20 na safe a gadar Olomore dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa tun farko an samu hadurra daban-daban guda biyu a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, inda mutum biyu suka rasa rayukansu.
Hadarin na Olomore, wanda shi ne na uku a yau, ya kai adadin wadanda suka mutu zuwa shida.
A cikin lamarin na Abeokuta, hukumar FRSC ta ce mutane uku ne lamarin ya shafa, suka hada da maza biyu da mace daya.
Florence Okpe, kakakin hukumar FRSC ta jihar Ogun, ta bayyana cewa matar da mutum daya sun mutu a hatsarin.
“An kai wanda aka jikkata Kuma an Kai su zuwa babban asibitin Abeokuta kuma an ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa na asibitin.
“Abinda ake zargin ya haddasa hatsarin shi ne gudun wuce kima wanda ya kai ga rasa yadda za a iya sarrafa motocin biyu”.
“Jami’an FRSC suna nan a kasa suna kula da lamarin,” Okpe ya shaidawa DAILY POST.