An samu tada jijiyan wuya da ƙwanji a Majalisar Wakilai ta Ƙasa a zaman ta na ranar Alhamis, akan shigowa da gurɓataccen Man fetur a Najeriya.
Majalisar ta yanke hukuncin bincike akan lamarin, tana mai cewa dukkanin jami’an gwamnati da aka samu da laifin shigowa da rarraba man fetur ɗin, dole su fuskanci hukunci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Jihar Zamfara Matawalle Ya Yi Ta’aziyya Ga Mataimakinsa Bisa Rasuwar Kawunsa
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC dana MRS Oil an ɗora masu tasowa alhaki akan lamarin.
Babban Manaja-Darakta na Hukumar NNPC Mele Kyari ya bayyana sunan Kamfanin Man Fetur na MRS da wasu guda uku akan laifin shigo da gurɓataccen Man Fetur a Najeriya.
Amma Kamfanin MRS a ranar Laraba ta musanta batun haɗa hannun ta shigowa da gurɓataccen man fetur ɗin, inda tace an hana shigowa dashi a Najeriya.