Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk ya bayyana cewa bazaiyi hawan Babbar Sallah, sakamakon rashin tsaro dake Fuskantar Jahar.
Wannan na kunshene a cikin wata sanarwa da Danejin Daura Alhaji Abdulmuminu Salihu a Madadin Sakataren Labaru na Masarautar.
Haka Zalika, Sanarwar tace a maimakon Haka, bayan Sallah, za’a gudanar da Addu’o’i na musamman, domin samun dauwamammen zaman lafiya da lumana a Jahar dama Kasa baki daya.
Idan dai ba’a manta ba Jaridar Dimokradiyya, ta kawo maku rahoton cewa, ko a Karamar Sallah data gabata, Masarautar ta dage hawan Sallah, sakamakon rashin tsaro dake addabar Jahar dama Kasa baki daya.