Gwamnatin Jahar Niger ta sanar da Mohammed Barau Kontagora a matsayin Sarki na bakwai na Kontagora.
Wannan na ƙunshene a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙananan hukumomi da Cigaban Al’umma Emmanuel Umar ya sanyawa hannu, aka rarraba wa manema labaru.
Idan dai za’a tuna an gudanar da taron zaɓar sarki na bakwai (Sarkin Sudan) na Kontagora a ranar Lahadi 19 watan Satumba na shekarar 2021, wanda masu zaɓen sarki suka yi a Masarautar Kontagora, a ƙarƙashin dokar data kafa masarautar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ebonyi: Wani Mutum Ya Kashe Matarsa,Dansa Da Adda Tare Da Raunata Wasu 6
Masu zaɓen sarkin a lokacin tattaunawar su da Gwamna Abubakar Sani Bello, sun tabbatar da cewa zaɓen sarkin ya biyo bayan dokar da aka shimfiɗa ta masarautar.
Haka zalika, matsayar an ɗauke ta ba tare da son kai ko kuma nuna ɓangaren ci.