Da Ɗuminsa: PDP ta lashe Ƙaramar Hukuma ta farko a Zaben Osun
An ayyana Sanata Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe Gwamnan Jahar Osun a Karamar Hukumar Atakumosa ta yamma.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP na zane APC a Zaɓen Osun – Adeyanju ya bayyana inda za’a iya yin Maguɗi cikin Dare
Ya samu ƙuri’u dubu 7,750 akan Dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar APC Gwamna Gboyega Oyetola wanda ya samu ƙuri’u dubu 6601 a zaɓen.
A cewar sakamakon da aka sanar a wurin tattara zaɓe na Ƙaramar Hukumar Atakumosa ta yamma, tana da mutane dubu 36,470, a yayinda aka tantance mutane dubu 15,171 a zaɓen.
Wani daga cikin wakilan Jam’iyyar yace akwai rikici a Mazaɓa ta 7, Akwati na 11, wanda ya sanya aka lalata akwati, da kuma zaben da ba’a kammala ba a wurin.