Sakataren Yaɗa Labaru na Kungiyar Ƴan Arewa ta ACF Yawe, ya rasu yana da Shekaru 65
Emmanuel Yawe Sakataren Yaɗa Labaru na Ƙungiyar Cigaban Siyasa ta Arewa ACF ya mutu yana da shekaru 65.
Wata ɗiyar sa Talatu ta tabbatar da labarin marar daɗi na mutuwar Mahaifin ta ga Wakilin Majiyar mu a Kaduna a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsaro: Kogi NSCDC ta horas da Jami’an ta akan yadda zasu yi aiki da Makaman su
A lokacin da take tabbatar da mutuwar Mahaifin ta, tace mahaifin ta ya rasu a baccin sa.
A lokacin da aka tambaye ta idan mutuwar Mahaifin ta da gaske ne, tace “eh dagaske ne. Bai tashi daga barci ba”.
Shima Sakatare-Janar na ACF Murtala Aliyu a lokacin da yake tabbatar da mutuwar Yawe, yace Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa ya kaɗu matuƙa a mutuwar.
Aliyu yace za’a sanar da lokacin binne shi a ƙanƙanin lokaci.
Ya bayyana cewar “muna sanar daku mutuwar Sakataren Yaɗa Labaru Chief Emmanuel Yawe da safe.
“Na sanar da Shugaban Ƙungiyar Audu Ogbeh, kuma ya bada umarnin in sanar da mambobin mu akan mutuwar.
Comments 1