Da Ɗuminsa: Tsohon Shugaban Sojojin Sama Saddique ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC a Bauchi
Tsohon Hafsan Sojin Saman Najeriya Air Marshal Abubakar Saddique ya lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC a Jahar Bauchi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sace Ƴar Takarar Majalisar Jaha ta APC a Jos
Kamar yadda rahoton ke nunawa ya lashe zaɓen da Ƙuri’u masu rinjaye da adadin yakai 370, akan ƴan Takarar da aka Fafata dasu a zaɓen.
Haka zalika, Ƴan Takara 7 ne suka Fafata dashi, amma ya samu nasarar doke su domin samun tikitin tsayawa takarar Gwamnan Jahar Bauchi.
Jam’iyyar APC dai ta ayyana ranar 26 ga watan Mayu na Shekarar 2022 a matsayin ranar da zata gudanar da zaɓen Fidda Gwani na Gwamna a Jam’iyyar.
Da yawa daga cikin Jahohin sun sanar da sakamakon Ƴan Takarar da suka samu nasarar lashe Kujerar Gwamnonin su, domin tun karar zaɓen 2023.
Comments 1