Yan majalisar dokokin jihar Imo sun sanar da tsige kakakin majalisar Paul Emeziem a safiyar yau Litinin.
Bayan sanar da tsige shugaban majalisar sai kuma suka sanar da nada Kennedy Ibe a matsayin wanda zai maye gurbin Hon. Paul.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano tayi alkawarin kammala aikin Janguza – Durum – Kabo – Karaye
Daukar wannan hukunci ta zo ne dai dai lokacin da aka jibge musu jami’an tsaro da gudun me kaje ya zo, yayin da 19 cikin yan majalisar 27 suka sanya hannu domin tsige shi.
Tsige shugaban ta zo ne bayan da aka tsige mataimakin kakakin majalisar, wanda kuma da saka hannun sa aka tsige kakakin.