Buba Galadima

Da A Ce Kotun Koli Ta Kwace Mulki Hannun Buhari Da ‘Yan Nijeriya Sun Yi Murna-Buba Galadima

Kakakin Kamfen din shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP wato Buba Galadima, ya ce da a ce kotun koli ta kwace kujerar shugabancin Nijeriya a hannun Buhari a ranar Laraba, da yanzu ‘yan Nijeriya suna ta murna.

Kotun koli a ranar Laraba, sun yi watsi da daukaka karar da PDP da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar ya yi yana mai kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kan tabbatar da zaben Buhari a matsayin shugaban kasar Nijeriya a zaben watan Fabarairu.

Da yake bayani a gidan Talabijin na Channel a ranar Laraba, Buba Galadima ya ce; “Da a ce hukuncin kotun a yau ya bayyana cewa ya cire Buhari daga ofishinsa, ina da tabbacin da yanzu ko’ina a fadin kasarnan ta rude saboda murna.”

Ya ci gaba da cewa; da al’umma sun yi ta murna ko ta ko’ina, suna zuba ruwa a kasa, suna bin tituna da kunna wuta suna murna, ya ce; “Shin ka ga wani da ya fito yana murna saboda hukuncin kotun yanzu?” ya tambaya.

A ranar Laraba ne, kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da PDP da kuma dan takararta Alhaji Atiku Abubakar  ya shigar yana mai kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kan tabbatar da zaben Buhari, inda mai Shari’a Tanko Muhammad wanda ya jagoranci wadansu membobi shida a kotun, suka yanke hukunci cikin kalmomi uku wanda ya kawo karshen takaddamar zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *