Shugaban kasar Madagascar, Andry Rajoelina a cikin jawabin da ya gabatar ya maida martani ga masu sukar kasarsa kan maganin gargajiya na cutar annobar Korona da suka ce sun gano.
Shugaban kasar ya maida wannan martanin ne a yayin da kafar watsa labarai ta France24 da RFI suke hira da shi, inda ya ce kasarsa za ta ci gaba da bunkasa maganin gargajiya na Korona saboda a cewarsa maganin ya warkar da al’ummar kasar da suka kamu bila’adadin.
“Muna da mutum 171 da suke dauke da cutar, inda mutum 105 suka warke bayan sun sha maganin gargajiyar na Koronar.” Ya tabbatar.
Ya ci gaba da cewa; da a ce ba kasar Madagascar ba ce ta samo maganin cutar Korona din, wata kasa ce daga Turai, “shin akwai wanda zai yi tantama ko ya karyata? Ban tunanin akwai…” inji shi.
Da yake maida martani bisa gargadin da WHO, ECOWAS, da kuma Cibiyar dake dakile yaduwar cututtuka masu yaduwa ta Afrika, CDC ta yiwa kasar Madagascar din, ya ce; sun yi hakan ne domin kashe guiwar kasarsa bisa maganin da suke son habbakawa, wanda ya ce ba za su taba yadda hakan ya faru ba.