Daga Khadija Mohammed
‘Yan sanda da sauran Jami’an tsaro sun kara tsananta tsaro tun a watan mayu biyo bayan da masu garkuwa suka kara matsanta garkuwa da suke yi da mutane wanda kusan kullum sai an samu labarin sacewa ko garkuwa da mutum.
Amma da Wakiliyarmu ta Samu zantawa da al’ummar Rijana, da Katari, mazauna garin sun sheda mana cewa wajen sati uku kenan, garkuwa da mutanen ya ragu.