Wani mai sharhi kan harkokin wasanni a jihar Kano Abdulkarim Abdullahi Tsoho ya ce da alama Qatar a gasar cin kofin duniya ba za ta kai labari ba.
Abdulkarim Tsoho yayin ganawarsa da Dimokuradiyya ya ce makamancin hakan ya faranta faruwa da kasar Afrika ta Kudu a shekarar 2010.
KARANTA ANAN: Ganduje Ya Bukaci Matasa Su Kauracewa Daukar Makami Yayin Kamfen
A wannan shekara Afrika ta kudu ce mai karbar bakunci, kuma tun a wasan rukunin farko ta fita daga cikin rukunin, kuma da alama hakan ce ke shirin faruwa ga kasar Qatar.
A wasan Lahadin nan na farko kuma na rukunin A, an fafata tsakanin Qatar mai masaukin baki, da kasar Ecuador, kuma aka tashi wasan Ecuador tayi nasara kan Qatar da ci 2 da nema.
Yanzu haka dai tuni Ecuador ta samu maki uku na wannan, yayin da zata sake fafatawa da kasar Senegal a wasa na gaba.
A wani labarin kuma: Mafita ga Matsalolin Najeriya Ita ce Zaɓen PDP a 2023 – Ayu
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi fatali da jam’iyyar APC domin samun damar farfaɗowa daga irin gashin ƙumar da APCn tayi musu.
Ayu wanda ya ce gwamnatin APC ta jawo sanya al’ummar kasar nan cikin mawuyacin hali, ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da lalata tattalin arzikin kasa.