- Da alamar ƙasar Italiya zata lashe kofin ƙasashen Turai
- Ƙasar Italiya ta lallasa ƙasar Swizalan da ci uku ba ko daya a jiya, inda yazama sune ƙasa ta farko data sami damar tsallake group stage.
- A shafin ESPN ruwaito Tun farko dai ƙasar italiyan ba’a sasu cikin ƙasashen da ake saran cin kofin, amma duba da irin rawar da suke takawa yazama abun mamaki.
Alessandro Del Piero yace “yanzu inada ƙwarin guiwar cin kofin.”
KARANTA:- Sergio Ramos ya bar kungiyar Real Madrid
Da dama jama’a sunta maka kudaden su wajan caca Kan cewa ƙasar Faransa ko Jamus sune zasu ci kofin.
A ranar Lahadi ne me zuwa zasu gwabza da ƙasar Wales Wanda zai bai daman zana saman tebur, wanda idan sunyi nasara zasu hadu da daya daga cikin ƙasashe biyu na Autriya Ko ƙasar Yukiren.
Amma sai dai mai horas da ƴan wasan kasar yayi bakin cikin samun matsalar ɗan wasan sa mai suna Chiellini wanda tun karon farko wasansu da Swizalan aka fidda shi waje baida lafiya.
Mai horas da ƴan wasan yace mai yiwuwa bazai ɗau dogon lokaci ba duba da irin ciwon da ya sameshi.
A WANI LABARIN:- Mai horas da yan wasan kasar Denmark ya ragargaji Uefa ne bisa nuna rashin ko’inkula kan batun Dan wasan.
Dan wasan kasar Denmark Erikson ya yanke jiki ya fada a tsakiyar wasa, inda nan take masu kula da lafiya suka haukansa don bincikan halinsa.
Mai horas da yan wasan yace akwai damar daga wasa awa 48 kamin a fara wasa idan akwai yiwuwar kamuwar yan Wasa da cutar numfashi, Amman idan cutar kwakwalwace hakan bazaiyuwu ba