Wata matashiya ‘yar shekaru 15 mai suna Safiya Sabon titi ta ayyana cewa; tana rayuwa ne cikin matsi da tsangwama, da rashin samun kulawar da ‘ya’ya ke bukata a wajen iyayen su.
Adan haka ta ce ba ta ga dalilin da zai maida ita gidan su da ta kauracewa da zama na tsawon kwanaki ba.
Safiyya ta shaidawa wakilin Hausa7 cewa; “Mahaifiyar ta ‘yar kasar Mali ce, a yanzu tana zaune ne a hannun marikiyar ta, wacce take kaka a gare ta”
Sai dai a cewar ta kakar na tafiya kasuwannin birnin Kano, inda take saka kwado ta kulle ta a gida, ba kudi ba abinci, ba’a ma ta batun ba laratu.
Ta kara da cewa, babban abinda ke damun ta shine jibga-jibgan samarin da ke shigo masu gida a kowanne lokaci, wanda sau tari sukan shafe tsawon lokaci a daki da kakar tata mai matsakaitan shekaru ba tare da tasan wainar da ake toyawa ba, wanda hakan ke barazana ga rayuwar ta, adan haka abinda tafi bukata a yanzu shine Aure, a cewar matashiya Safiyya Sabon titi.