Daga: Mustapha Musa Sarkin Pawa
Wani mai sana’ar dakon rake a yankin karamar hukumar Lere Mai suna Dahiru Ya’u, ya bayyana irin alfanun da ya ke samu a sana’ar ta shi.
Dahiru Ya’u ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da Wakilin Jaridar Dimokuradiyya a Karamar hukumar Lere dake jihar Kaduna.
Inda ya bayyana cewa, sana’rar ta su tanada wahala sosai, amma idan mutum ya daure kuma ya saba, ba zai ga wahalar ta ba, domin su yanzu ko ganin wahalar aikin ba sa yi.
Ya kuma bayyana wa Jaridar Dimokuradiyya yadda aikin nasu yake gudana kamar haka;
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sunyi Garkuwa da Wani Hamshakin Dan Kasuwa a Jihar Taraba
“A na kai mu gonar rake, sai mu sare, sai kuma wani ma’aikacin yazo ya shirya, sannan mu daure kamar yadda kake gani, dauri uku akewa kone dami, sannan sai mu dauka mu Kai shi inda ake ajewa” inji shi.
Ko nawa kuke iya samu a kullum?
Dahiru Ya’u ya ce, “Ya danganta da yanayin aikin wata rana aikin dayawa, Kazalika wata rana kuma babu yawa, amma a kalla muna samun dubu uku, dubu hudu ko dubu biyu wani lokacin” a cewar shi.
“Gaskiya muna samun albarka sosai da wannan sana’ar, domin kuwa da ita nayi Aure, na gina gida, nasai mashin, kuma nake biyawa kanina kudin makaranta yana poly a Zaria.” Kamar yadda ya bayyana.
Duba da wannan aikin na karfi ne shin ko kuna anfani da wasu kayakin kara kuzari?
Dahiru ya ce “A’a ni dai banasha komai, amma kila baza’a rasa masu sha ba, hasalima ni na tsani shaye shaye a rayuwa ta”
Kazalika ya Kuma bayyana cewa, “Inna kira ga matasa da su daina zaman banza, su kama sana’a, domin su dogara da kansu, kuma su rufawa kansu asiri, harma su taimaki iyaye da ‘yan’uwansu da sauran jama’a”
A karshe ya Kuma yi kira ga gwamnati da ta taimakawa mata harda wadanda ba su yi karatu ba, domin tallafawa matasa, Wanda hakan ne zai ragewa kasarnan radadin da ta ke fuskanta na matsalar tsaro, da sauran damuwoyin dake damu kasarnan.
Comments 1