Labarin dake shigowa Dimokuradiyya a halin yanzu na nuni da cewa; majalisar dokokin jihar Legas ta zartar da dokokin Haraji da ta hana kiwo a fadin jihar.
Dama tuni kudurin dokar ya zarce karatu na farko da na biyu, inda kwamitin kudi aka sanya shi ya kawo rahoto a yau Alhamis.
A jiya Laraba, kwamitin ya gudanar da taron jin ra’ayin al’umma akan kudirin dokar, inda a yau Alhamis aka mika wa majalisar dokokin jihar sakamakon rahoton.
Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa, ya bai wa mukaddashin magatakardar majalisar, Mista Olalekan Onafeko, da ya bai wa Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu takardar dokar.
An zartar da kudurorin dokokin guda biyu bayan an karanta su a karo na uku a zauren majalisar da bayan da ‘yan majalisar baki daya suka sanyawa kuri’arsu ga kudirin dokar a zauren.