Hukumar da ke yaki da fasa-kwauri a Nijeriya ta ce za a ci gaba rufe kan iyokokin kasar da ke tudu har zuwa lokacin da Nijeriyar za ta samu cikakken hadin kai daga sauran kasashen da take makwabtaka da su.
Hukumar Kwastam ta ce harkokin tsaro da na tattalin arziki sun inganta a Nijeriya sakamakon rufe iyakokin kasar da ke kan tudu.
Kanar Hamid Ali mai ritaya shi ne shugaban hukumar, kuma ya yi wa Ibrahim Isa na Bbc Hausa karin bayani.