Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya tsallake rijiya da baya a yayin da ‘yan bindiga suka kai hari a wurin da ake gudanar da zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kogi. Gwamna Fintiri a matsayinsa na shugaban kwamitin shirya zaben ya kasance a wurin domin tabbatar da an gudanar da zaben cikin zaman lafiya.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa; maharan sun kawo hari ne da misalin karfe 1:45 na dare inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi. A cewar ganau, tuni aka kirga kuri’un akwati takwas cikin goman da aka kada kuri’a, kafin ‘yan bindigar su zo su tarwatsa taron.
Ya zuwa hada wannan rahoton ba a tabbatar da ko an samu raunuka ko asarar rai ba.