Rahotanni dake shigowa Jaridar Dimokuradiyya a halin yanzu ya nuna cewa; an tsige Honurabul Mohammed Gwampo a matsayin Kakakin majalisar jihar Taraba.
Gwampo wanda yake dan majalisa ne mai wakiltar yankin Yorro, an tsige shi ne a yayin wani zama a yau Litinin.
‘Yan majalisar sun nada Honorabul Charles Maijankai mai wakiltar yankin Karim Lamido I a matsayin sabon mataimakin Kakakin majalisar.
Maijankai kafin nada shi a sabon mukamin, shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar.
Bukatar cire mataimakin Kakakin majalisar ya fito ne daga tsohon shugaban masu rinjayen majalisar, Honorabul Albasu Kunini mai wakiltar yankin Lau a jihar.