Kotun zaben shugaban kasa ta yi watsi da zargin cewa dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba haifaffan daijeriya bane kuma bai cancanci takaran zabe. Wannan hukunci ya biyo bayan ikirarin APC da shugaba Muhammadu Buhari cewa Atiku ba haifaffen dan Nijeriya bane saboda a lokacin da aka haifeshi, garin Jada ba ta cikin Nijeriya, tana kasar Kamaru. A hukunci na shida da kotu ta yanke, ta ce ba tada hurumin tabbatar da ko rashin tabbatar da cewa dan takara bai cancanta ba.
Sauran hukunce-hukuncen da aka yanke a yau sune kotun ta yi watsi da ikirarin jam’iyyar PDP da Atiku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen magudin zabe. Kotun ta ce ba zai yiwu PDP da Atiku ce jami’an tsaro sun yi magudi kuma ta manta da su lokacin shigar da kara.
Alkalin kotun ya soke dukkan bukatar da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta gabatar na watsi da karar jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar. Hukumar INEC ta bukaci kotun zaben ta yi watsi da karar PDP saboda daya daga cikin lauyoyinta, Dakta Livy, ba sahihin lauya bane. Hakazalika INEC ta bukaci kotu ta soke bukatar PDP da Atiku na cewa shugaba Buhari bai cancanci yin takara a zabe ba.