Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasa a gobe Talata, 1 ga watan Oktoba, da misalin karfe 7 na safe.
Jawabin da shugaban kasar zai yi yana daga cikin bukukuwan tunawa da ranar ‘yancin kai, wanda yanzu Nijeriyar ta cika shekara 59 da samun ‘yancin kai.
Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa sa ya fitar, inda ya ce shugaban zai yi jawabin ne a gidajen Talabijin na NTA da Rediyo na gwamnati. Inda ya bukaci sauran kafafen watsa labarai da su bibiyi wadannan kafafe domin samun jawabin shugaban kasar.